Maganin hana karyewar gashi
Abubuwan dake haddasa Karyewar gashi sun hada da yawan damuwa, zafi, ciwo me tsanani irin su ciwon suga, hawan jini da sauransu.
A wannan rubutu zamu yi cikakken bayani game da karyewar gashi da maganin hana karyewar gashi.
Bushewar gashi da barinshi ba gyara ma yana sawa ya rika kakkaryewa.
Ga cikakken bayani kamar haka game da abubuwan dake kawo karayar gashi:
Abinci: Kalar abincin da ake ci na taimakawa matuka wajan kyawun gashi da kuma hana karyewarsa. Kalar abincin dake taimakawa wajan hana karyewar gashi sune, dafaffen kwai, gasashshiyar kaza, ganye irin su kabeji, dodon kodi, madara, da Yegot.
Yawan Damuwa: Kasancewa cikin yawan damuwa na sanya karyewar gashi. Dan haka, masana sun bada shawarar a rika cire kai daga cikin damuwa dan samun gashi me kyau da baya karyewa....