Maganin ciwon kai kowane iri
Ciwon kai na da magunguna na turawa wanda suke aiki da kyau, musamman idan ba me tsanani bane sosai.
Magungunan dake magance ciwon kai sun hada da.
Aspirin
Paracetamol
da Ibuprofen.
Hakanan masana sunce kwanciya a cikin daki me duhu, wanda babu hasken wutar lantarki ko na rana na taimakawa wajan magance matsalar ciwon kai.
Abincin da ake son me yawan ciwon kai ya rika ci:
Nama
Ganye, irin su Kabeji, Zogale da sauransu.
Gyada.
Madara.
Kwai.
Ana kuma amfani da wadannan dabarun na kasa dan magance matsalar ciwon kai:
Amfani da tsumma me sanyi a dora a goshi.
Ko Amfani da tsumma me dumi a dora a goshi ko a bayan kai.
Ana amfani da Ganyayyaki da aka saka a firjin suka yi sanyi.
Ana iya yin wanka da ruwan sanyi.
Hasken wutar lantarki, Hasken ...