Ya ake farantawa saurayi rai
A na farantawa saurayi raine ta hanyar damuwa da shi.
Damuwa dashi na nufin damuwa da abinda yakeyi musamman Wanda ya baki labari, idan ya baki labarin Abu, kasuwanci ne, aiki ne, ko wani Abu da yakeyi, ki nuna damuwa akai, ki rika tambayarsa ya ake ciki da abunnan daga lokaci zuwa lokaci.
Kuma kamar yanda idan ya yabeki kike jin dadi, idan ya gaya miki yana sonki kike jin dadi, to haka shima idan kina son ki faranta masa, ki rika yabonsa, da gayamai irin soyayyar da kike masa.
Yana da kyau ki rika nuna kishinsa, amma kada ki wuce gona da iri, hakanan ki rika tambayarsa 'yan gidansu da yanda suke.
Ki rika nuna mai kaguwa da soyuwar kasancewa tare dashi da son ya aureki dan Ku yi rayuwa tare.
Idan ya miki kyautar dubu 1, ki nuna jin dadi da mai godiya kamar ya miki kyautar du...