fbpx
Wednesday, July 6
Shadow

Wasanni

Da Dumi Duminsa: Lionel Mesai zai fice daga Paris Saint Germain

Da Dumi Duminsa: Lionel Mesai zai fice daga Paris Saint Germain

Breaking News, Wasanni
Kungiyar Paris Saint Germain na shirin sayar da Lionel Messi a wannan kakar, cewar dan jaridar kasar Sifaniya, Pedro Morata. Messi ya koma PSG ne a kakar bara daga Barcelona amma sai dai tauraruwarsa bata haskaka a gasar ta Ligue one ba, inda yaci kwallaye 11 kacal a wasanni 34 daya bugawa PSG. Kuma dan wasan daya lashe kyautar Ballon D'or bakwai ya nuna kwazonsa a kwanakin nan inda ya taimakawa kasarsa ta Argentina ta lashe kofin Finalissima. Kuma yaci kwallaye da dama, yayin shi kuma darektan PSG, Luis Campus yake shirin sayar da shi don yanaso ya gina tawagar kungiyar.
Victor Osimhen zai iya zama zakaran dan wasan duniya, cewar Drogba

Victor Osimhen zai iya zama zakaran dan wasan duniya, cewar Drogba

Wasanni
Tsohon tauraron dan wasan kasar Ivory daya taka leda a kungiyar Chelsea, Didier Drogba ya bayyana cewa dan wasan Najeriya Oshimhen zai iya zama zakaran duniya a gasar tamola. Drogba yace dan wasan mai shekaru 23 dake taka leda a Napoli zai iya zama zakaran gwaji a harkar tamola nan gaba kadan. Osimhen yayi nasarar ciwa Napoli kwallaye 14 kuma ya taimaka wurin cin biyar a kakar bara.
Mohammed Salah ya sabunta kwantirakinsa na tsawon shekaru uku a Liverpool

Mohammed Salah ya sabunta kwantirakinsa na tsawon shekaru uku a Liverpool

Wasanni
Tauraron dan wasan gaba na kungiyar Liverpool dan kasar Misra, Mohammed Salah ya sabunta kwantirakinsa na tsawon shekaru uku. Liverpool ta dauki lokaci mai tsawo kafin ta shawo kan Mohammed Salah ya sabunta kwntirakin. Inda har wasu rahotanni suka fara cewa shima zai bi sahun Sadio Mane ya sauya sheka a wannan kakar. Amma sai dai yanzu ta faru ta kare kuma yace zai cigaba da taimakawa kungiyar ta lashe kofuna.
Da Dumi Duminsa: Sabuwar kungiyar da Ronaldo zai koma a mako mai zuwa ta bayyana

Da Dumi Duminsa: Sabuwar kungiyar da Ronaldo zai koma a mako mai zuwa ta bayyana

Breaking News, Wasanni
Tsohon dan wasan kasar Itiliya, Angele di Livio ya bayyana kungiyar da tauraron dan wasan Manchester United zai koma a mako mai zuwa. Inda yace Cristiano Ronaldo zai koma kungiyar Roma a mako mai zuwa ranar bakwai ga watan Yuli. Di Livio ya bayyana cewa Roma ta jima taba harin sayen dan wasan bayan Mourinho ya fara horas da ita, kuma Mourinho ya horsa da Ronaldo a Madrid.
Sunayen ‘yan wasa bakwai da kocin Manchester United ya cewa su sauya sheka a wannan kakar

Sunayen ‘yan wasa bakwai da kocin Manchester United ya cewa su sauya sheka a wannan kakar

Wasanni
Saboon kocin Manchester Unies na cigaba da gina kungiyar don ganin cewa yayi nasara ba kamar Ole Gunnar da Jose Mourinho data kora ba. Inda yake cigaba da harin sayen 'yan wasa kuma yake sayar da wasu 'yan wasan nashi. Paul Pogba, Cavani da sauransu duk sun bar kungiyar kuma kocin yanzu ya fadawa 'yan wasa biyar cewa su san inda dare yayi masu. Wanda suka hada da Henderson, Axel Tuanzebe, Phil Jones, Eric Bailly, Alex Telles, Brandon Williams da Andreas Pereira.
Milyoyin kudin da PSG zata ba kocinta Pochettino don ya sauya sheka sun bayyana

Milyoyin kudin da PSG zata ba kocinta Pochettino don ya sauya sheka sun bayyana

Wasanni
Makudan kudaden da kungiyar Paris Saint Germain zata ba kocinta Mauricio Pochettino bayan ya amince ya bar kngiyar sun bayyana. PSG bata son kocin ya cigaba da horas da 'yan wasanta wanda hakan yasa ta bukaci ya suya sheka, amma yace dole sai ta biya shi saboda yana sauran kwantirakin shekara guda. Wanda hakan yasa ta amince ta biya shi yuro miliyan goma don ya hakura da kwantorakin nashi daya rage. Kocin kungiyar Nice, Christophe Galtier ne zai cigaba da horas da PSG, bayan Pochettino ya kasa taimakawa kungiyar ta lashe kofin Lig 1 a kakar data gabata.
Za’a ba wanda ya lashe gasar tseren Marathon dala 80,000 a jihar Abuja

Za’a ba wanda ya lashe gasar tseren Marathon dala 80,000 a jihar Abuja

Breaking News, Wasanni
A ranar 17 ga watan disemba za'a gudanar da tseren gudu na Marathon a babban birnin tarayya Abuja, cewar wa'yanda suka tsara tseren. Shugaban kungiyar data tsara tseren, Femi Abegunde ne ya bayyana hakan ranar talata, Kuma yace mutane 60 ne zasu yi wannan gasar hadda 'yan kasar waje ma zasu shiga a fafata dasu. Yayin da za'a baiwa wanda ya lashe gasar kyautar dala 80,000 wanda yayi daida da naira 48,800,000. Kuma za ayi gudun ne na kilo meter 42  fadin babban birnin tarayyar.
Shalelen PSG, Mbappe ya cewa kungiyar ta sayar da Neymar don baya cikin tsarinsa

Shalelen PSG, Mbappe ya cewa kungiyar ta sayar da Neymar don baya cikin tsarinsa

Breaking News, Wasanni
Kungiyar Paris Saint Germain ta cewa daya daga cikin zakarun 'yan wasanta cewa zai iya barin kungiyar a wannan kakar, watau Neymar. Jigon kungiyar kuma shalelenta, Mbappa ne yace baya son shi a kungiyar saboda yana so su gina sabuwar tawaga don cigabansu kuma Neymar a cikin tsarin shi. Saboda haka sun fadawa mahaifin dan wasan Brazil din cewa zasu sayar da shi ko kuma su samar masa wata kungiyar da zasu ba aron shi don har yanzu yanada sauran kwantirakin shekaru uku a PSG.