Wednesday, January 15
Shadow

Labaran Falasdinawa

Kasashen Larabawa sun sha Alwashin ba zasu bar Falas-dinawa su sake mallakar makamai ba bayan yakin su da Israela

Kasashen Larabawa sun sha Alwashin ba zasu bar Falas-dinawa su sake mallakar makamai ba bayan yakin su da Israela

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Yakin gaza da isra'ila
Rahotanni sun bayyana cewa, kasashen Larabawa sun dauko alwashin ba zasu sake barin Falas-dinawa au mallaki makamai ba bayan an gama yaki tsakaninsu da Israela. Hakan na zuwa ne yayin da ake tsammanin za'a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Israela da Kungiyar Hamas. Saidai abin tambaya anan shine, anya kasashen Larabawan zasu iya aikata hana Falas-dinawa mallakar makamai? Dalili kuwa shine a yanzu gashi ana ta kashesu babu kasar Larabawan data shigar musu ko ta tsaya musu, an zura ido ana kallo Israela na musu kisan kare dangi, ta yaya zasu yadda a hanasu mallakar makamai bayan sun san duk randa Israela ta sake far musu da yaki babu me tare musu? Wannan dai abune me kamar wuya.
Biden ya yi kira ga Isra’ila da Hamas su amince da sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta

Biden ya yi kira ga Isra’ila da Hamas su amince da sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Yakin gaza da isra'ila
Shugaba Biden na Amurka ya yi kira ga Isra'ila da Hamas su amince da sabuwar yarjejeniyar tsagaita a yakin da suke yi tsakaninsu. Yarjejeniyar za ta sa jami'an Isra'ila su tsagaita wuta ta tsawon mako shida, sannan Hamas ta saki Isra'ilawan da ta yi garkuwa da su - a kuma saki Falasdinawan da ake tsare da su a gidajen yari a Isra'ila. Yarjejeniyar ta yi tanadin Isra'ila za ta janye daga yankunan Gaza sannan ta kyale a rika shiga da kayayyakin agaji. Yayin da za a a ci gaba da tattaunawa, yarjejeniyar za ta ci gaba da aiki har a kai ga sakin duka wadanda aka yi garkuwa da su. Daga nan dakarun Isra'ila su fice daga Gaza Falasdinawa su koma gidajensu su ci gaba da rayuwa.
Yanzu-Yanzu:Kasar Faransa ta hana kasar Yahudawan Israela zuwa bikin nuna makamai saboda kisan Falas-dinawa

Yanzu-Yanzu:Kasar Faransa ta hana kasar Yahudawan Israela zuwa bikin nuna makamai saboda kisan Falas-dinawa

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Yakin gaza da isra'ila
A karin farko, Kasar Faransa ta zama kasar Turai ta farko data kakabawa kasar Israela takunkumi kan kisan kiyashin da takewa falasdinawa. Faransar ta hana kasar Israela hakartar bikin nuna makamai da za'a yi ranar 17 zuwa 21 ga watan Yuli. Bikin dai shine bikin nuna ko kuma bajakolin makamai mafi girma a Duniya wanda aka sakawa sunan Eurosatory 2024. Wannan mataki na zuwane bayan da kasar Israela ta ki bin umarnin kotun Duniya na daina kashe Falasdinawa. Hakanan kasashen Duniya da yawa na ta Allah wadai da kasar kan kisan da takewa Falas-dinawan. Sannan kuma wannan mataki zai iya zama gargadi ga kasar ta Israela ta canja salo ko kuma akwai yiyuwar wasu sauran kasashen Turawa suma su saka mata takunkumo.
Kalli Bidiyo yanda dan majalisar kasar Faransa ya daga tutar Falas-dinawa a yayin zaman majalisar

Kalli Bidiyo yanda dan majalisar kasar Faransa ya daga tutar Falas-dinawa a yayin zaman majalisar

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Yakin gaza da isra'ila
Dan majalisar kasar Faransa, Sébastien Delogu ya daga tutar Falas-dinawa a farfajiyar majalisar yayin da ake zaman zauren majalisar. Dan majalisar yace kasarsa ta Faransa na da hannu a kisan kare dangin da Israela kewa Falas-dinawa ta hanyar sayarwa da Israelan makamai. Yayi kira ga shugaban kasar, Emmanuel Macron da ya daina sayarwa da Israela makamai. https://twitter.com/sahouraxo/status/1795457671119688144?t=h0iwUNItfTYrx_DDpFfIbA&s=19 Saidai an dakatar dashi sannan aka bashi dakatarwar kwanaki 15. Saidai bayan dakatar dashi, Dan majalisar ya shiga cikin masu zanga-zangar goyon bayan kasar ta Falas-dinawa a kan titi: https://twitter.com/sahouraxo/status/1795788298402557952?t=QXi2U6P3vslbvkahEq1zIA&s=19 Saidai a wani lamari kuma na ban mamaki, shine, kaka...
Hotuna da Bidiyo:Zanga-zanga ta barke a kasar Mexico inda ‘yan kasar suka fito suna goyon bayan Falasdinawa, sun yi yunkurin kona ofishin jakadancin kasar Israela

Hotuna da Bidiyo:Zanga-zanga ta barke a kasar Mexico inda ‘yan kasar suka fito suna goyon bayan Falasdinawa, sun yi yunkurin kona ofishin jakadancin kasar Israela

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Yakin gaza da isra'ila
Mutane akalla 200 ne suka fito a kasar Mexico inda suke nuna rashin jin dadi kan kisan da kasar Israela kewa Falas-dinawa. Mutanen sun yi arangama da jami'an tsaro inda suka rima jefawa jami'an tsaron duwatsu da wuta da suka kunna a tsumma. https://twitter.com/Megatron_ron/status/1795769204068491650?t=8ik7IoPGe4o8qQNpnKQYmA&s=19 Saidai jami'an tsaron suma sun rika jefawa masu zanga-zangar barkonon tsohuwa da kuma duwatsu.
Kasar Saudiyya ta zuciya akan Israela inda tace Israelan na aikatawa Falas-dinawa kisan kare dangi

Kasar Saudiyya ta zuciya akan Israela inda tace Israelan na aikatawa Falas-dinawa kisan kare dangi

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Yakin gaza da isra'ila
Kasar Saudiyya ta yi Allah wadai da kisan da kasar Israela kewa Falas-dinawa. Ta bayyana cewa Israelan nawa Falas-dinawan kisan kare dangi. Israela ta kashe mutane akalla 21 a harin data kai kan al-Mawasi dake Rafah. Hakan ya zo ne bayan da ta kashe mutane sama da 40 a harin data kai kan wani sansanin a Rafah ranar Labadi. Ma'aikatar harkokin waje ta Kasar Saudiyya tace Israela ce ke da alhakin koma menene ke faruwa a Rafah. Kuma ta yi kiran kasashen Duniya da su dauki matakin hana wannan kisa da Israela kewa Falasdinawan.
Da Duminsa: Kungiyar kasashen Turai tace a kakabawa Israela takunkumi saboda kisan kiyashin da takewa Falas-dinawa

Da Duminsa: Kungiyar kasashen Turai tace a kakabawa Israela takunkumi saboda kisan kiyashin da takewa Falas-dinawa

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Yakin gaza da isra'ila
A karshe dai, kasashen Tarayyar Turai karkashin EU sun juyawa kasar Israela baya. Kasashen sun fito sun nemi a kakabawa kasar Israela takunkumi saboda kisan kiyashin da takewa Falas-dinawa. Hakan ya biyo bayan nacewa da kasar ta yi cewa sai ta shiga Rafah inda dubban fararen hula na Falasdinawa ke gudun Hijira. Kasar kuma ta kai wani mummunan hari a sansanin 'yan gudun hijirar wanda ya kone mutane akalla 50 kurmus ciki hadda yara kanana. Lamarin ya jawowa kasar Israela Allah wadai wanda daga baya Firaministan kasar, Benjamin Netanyahu ya fito yace kuskurene kuma suna bincike akai.
Firaministan Israela, Benjamin Netanyahu yace harin da sojojin kasarsa suka kai a Rafah kuskurene

Firaministan Israela, Benjamin Netanyahu yace harin da sojojin kasarsa suka kai a Rafah kuskurene

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Yakin gaza da isra'ila
Firaministan Israela Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa, harin da suka kai kan sansanin 'yan gudun Hijira wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 50 kuskurene. Ya bayyana hakane amma kuma yace zasu ci gaba da yaki dan tabbatar da sun samu nasara akan 'yan ta'dda. Ya bayyana cewa amma kuma sun san cewa kuskurene harin da suka kai kuma suna bincike akan lamarin. Harin dai ya fuskanci Allah wadai daga bangarori daban-daban na Duniya.
Yanzu-Yanzu: Yaki ya barke tsakanin sojojin Israela dana kasar Misra/Egypt

Yanzu-Yanzu: Yaki ya barke tsakanin sojojin Israela dana kasar Misra/Egypt

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Yakin gaza da isra'ila
Rahotanni da muke samu daga gabas ta tsakiya na cewa, yaki ya barke tsakanin sojojin kasar Israela dana Misra/Egypt. Lamarin ya farune a daidai Rafah, kaamar yanda kafar Aljazeera ta ruwaito. A baya dai dama kasar ta Misra/Egypt ta gargadi Israela kada ta kai sojojinta yankin Rafah, saidai Israela ta yi kunnen uwar shegu da wannan gargadi indaa ta kai sojojin nata wajan. Biyo bayan hakan itama Misra/Egypt ta jibge sojojinta a iyakarta ta Rafah. To a yanzu dai yaki ya barke kamar yanda muke samun bayanai. Rahoton yace sojojin Misra/Egypt ne suka fara budewa na Israela wuta inda suma na Israelan suka mayar da martani. Saidai zuwa yanzu dai babu rahoton jikkata ko kuma rasa rai.