Tuesday, January 14
Shadow

Yakin gaza da isra’ila

Da Duminsa: Kungiyar kasashen Turai tace a kakabawa Israela takunkumi saboda kisan kiyashin da takewa Falas-dinawa

Da Duminsa: Kungiyar kasashen Turai tace a kakabawa Israela takunkumi saboda kisan kiyashin da takewa Falas-dinawa

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Yakin gaza da isra'ila
A karshe dai, kasashen Tarayyar Turai karkashin EU sun juyawa kasar Israela baya. Kasashen sun fito sun nemi a kakabawa kasar Israela takunkumi saboda kisan kiyashin da takewa Falas-dinawa. Hakan ya biyo bayan nacewa da kasar ta yi cewa sai ta shiga Rafah inda dubban fararen hula na Falasdinawa ke gudun Hijira. Kasar kuma ta kai wani mummunan hari a sansanin 'yan gudun hijirar wanda ya kone mutane akalla 50 kurmus ciki hadda yara kanana. Lamarin ya jawowa kasar Israela Allah wadai wanda daga baya Firaministan kasar, Benjamin Netanyahu ya fito yace kuskurene kuma suna bincike akai.
Firaministan Israela, Benjamin Netanyahu yace harin da sojojin kasarsa suka kai a Rafah kuskurene

Firaministan Israela, Benjamin Netanyahu yace harin da sojojin kasarsa suka kai a Rafah kuskurene

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Yakin gaza da isra'ila
Firaministan Israela Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa, harin da suka kai kan sansanin 'yan gudun Hijira wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 50 kuskurene. Ya bayyana hakane amma kuma yace zasu ci gaba da yaki dan tabbatar da sun samu nasara akan 'yan ta'dda. Ya bayyana cewa amma kuma sun san cewa kuskurene harin da suka kai kuma suna bincike akan lamarin. Harin dai ya fuskanci Allah wadai daga bangarori daban-daban na Duniya.
Yanzu-Yanzu: Yaki ya barke tsakanin sojojin Israela dana kasar Misra/Egypt

Yanzu-Yanzu: Yaki ya barke tsakanin sojojin Israela dana kasar Misra/Egypt

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Yakin gaza da isra'ila
Rahotanni da muke samu daga gabas ta tsakiya na cewa, yaki ya barke tsakanin sojojin kasar Israela dana Misra/Egypt. Lamarin ya farune a daidai Rafah, kaamar yanda kafar Aljazeera ta ruwaito. A baya dai dama kasar ta Misra/Egypt ta gargadi Israela kada ta kai sojojinta yankin Rafah, saidai Israela ta yi kunnen uwar shegu da wannan gargadi indaa ta kai sojojin nata wajan. Biyo bayan hakan itama Misra/Egypt ta jibge sojojinta a iyakarta ta Rafah. To a yanzu dai yaki ya barke kamar yanda muke samun bayanai. Rahoton yace sojojin Misra/Egypt ne suka fara budewa na Israela wuta inda suma na Israelan suka mayar da martani. Saidai zuwa yanzu dai babu rahoton jikkata ko kuma rasa rai.
Rahotanni sun ce, Israela ta kashe Falasdinawa 50 a wani mummunan hari data kai Rafah, Kalli Bidiyon yanda mutane suka kone kurmus

Rahotanni sun ce, Israela ta kashe Falasdinawa 50 a wani mummunan hari data kai Rafah, Kalli Bidiyon yanda mutane suka kone kurmus

Duk Labarai, Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Yakin gaza da isra'ila
Rahotanni sun nuna yanda Israela ta kai wani mummunan hari a wajan sansanin 'yan gudun Hijira dake Rafah. Harin yayi sanadiyyar wuta ta tashi a sansanin inda mutane akalla 50 suka kone kurmus. An ta ganin gawarwakin mutane sun kone ana zakulosu a bidiyon da suke ta yawo a shafukan sada zumunta. Saidai hakan na zuwane bayan da kotun majalisar dinkin Duniya ta baiwa Israelan umarnin daina kai hari Rafah: https://twitter.com/CensoredMen/status/1794815544425873773?t=YnxpkOAzQnE8MDsF5KvKOg&s=19 https://twitter.com/syylllia/status/1794855529753506121?t=vZml1Ho1zA4AK7Yvdj7yew&s=19 https://twitter.com/jacksonhinklle/status/1794824350195167660?t=5qymwlqoX0GFP57gJcujrQ&s=19 Abin jira a gani shine wane mataki majalisar dinkin Duniyar zata dauka tunda dai gashi I...