Tuesday, February 24
Shadow

DA DUMIDUMINSA: Kotu Ta Tura Mawaƙi Surajo Mai Asharalle Zuwa Gidan Yari a jihar Katsina

Daga Comr Nura Siniya

Wata Kotu ta tura fitaccen mawaƙin Asharalle a jihar Katsina Alhaji Surajo Mai Asharalle zuwa gidan gyaran hali har ya zuwa lokacin da za a cigaba da shari’a akan zargin da ake masa na harbin wasu jami’an hukumar Hisba a jihar Katsina

Majiyar tace lauya mai kare Alhaji Surajo mai Asharalle, ya ce kotu ta dage shari’ar zuwa ranar Alhamis 10 ga Aprilu 2025 domin ci gaba da sauraren kara.

An dai zargi Alhaji Surajo mai Asharalle da ya’yansa biyar da yin harbi a lokacin rikicinsu da Hukumar Hisba a gidansa dake ƙofar Ƙaura a jihar Katsina.

Karanta Wannan  Matatar man fetur ta Dangote ta rage farashin man fetur dinta da Naira 30

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *