Wednesday, April 8
Shadow

Da Duminsa: Gwamnatin tarayya ta kawo tsarin hawa jirgin sama bashi, daga baya mutum ya rika biya a hankali

Gwamnatin tarayya ta hanyar (CREDICORP) ta kawo tsarin hawa jirgin sama bashi yanda mutum zai rika biya a hankali.

(CREDICORP) ce ta sanar da hakan a shafinta na X inda kuma tace ta yi wannan shiri ne da hadin gwiwar manhajar MyVisaro, idan mutum na bukatar hawa jirgin da gaggawa bashi da kudi, kawai zai shiga manhajar MyVisaro ne ya bayyana aniyarsa.

Saidai akwai tantancewa, dan tabbatar da mutum ya cika wasu sharuda kamin bashi damar hawa jirgin kyauta.

Gwamnatin tace ta kawo wannan tsari ne dan saukakawa ‘yan Najeriya musamman ma a yayin da wata tafiya ta gaggawa ta samesu.

Karanta Wannan  Saidu Mohammed ya karbi shugabancin hukumar NMDPRA daga hannun Farouk Ahmed

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *