
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya fasa karawa Dogarinsa, Yusuf Nurudeen girma daga mukamin Colonel zuwa Brigadier General.
A watan Janairu da ya gabata ne dai aka kara masa girma zuwa Colonel.
Inda a yanzu kuma ake son kara masa girma zuwa Brigadier General.
Amma a doka sai ya shekara 4 yana mukamin Colonel kamin ya je yayi wata horaswa sannan a kara masa mukamin zuwa Brigadier General.
Saidai Shugaba Tinubu ya so ya masa karin girman ba tare da bin waccan matakai ba.
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, wasu tsaffin janarorin sojane suka shiga maganar shiyasa aka fasa karin mukamin da aka shirya yi ranar Litinin.