Monday, December 16
Shadow

Da Duminsa: Shugaban Sojojin Najeriya ya mutu

Kakakin shugaban kasa,Bayo Onanuga ya tabbatar da mutuwar shugaban sojojin kasa na Najeriya, Lt. General Taoreed Abiodun Lagbaja.

Shugaban kasar ya bayyana cewa cikin takaici da alhini yana sanar da mutuwar shugaban sojojin kasa na Najeriya, Lt. General Taoreed Abiodun Lagbaja.

Ya mutu ne yana da shekaru 56.

Sanarwar tace ya mutu ne a daren ranar Talata a Legas bayan wata rashin lafiya.

An haifeshi a shekarar February 28, 1968 kuma shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya nadashi Shugaban sojojin Najeriya ranar June 19, 2023.

Karanta Wannan  Kasar Faransa tace ta daina sayarwa da kasar Israela makakai saboda kashe Falasdinawa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *