
Ginin Aji ya fadawa dalibai mata a makarantar mata ta Government Girls Science Technical College, Potiskum dake jihar.
Lamarin ya farune yayin da ake tsaka da karatu kamar yanda rahotanni suka bayyana wanda yayi sanadiyyar dalibai da yawa suka makale a karkashin gini.
Mutane da yawa ciki hadda malaman makarantar sun kaiwa daliban daukin gaggawa.
An garzaya da daliban da suka jikkata zuwa Asibitin dake garin Fataskum.
zuwa yanzu dai suna karbar kulawa ta musamman daga likitoci.