
Wata babbar fasta da aka rubuta salatin Annabi Muhammad SAW a jikinta a kasar Ingila ta firgita turawan kasar.
Wani baturene ya fara ganin fastar inda ya tambaya me zai gani haka a kasarsa?
An tafka mahawara sosai akan lamarin wanda ya dauki hankula sosai a kafafen sadarwar zamani.