
Matatar man fetur ta Dangote ta dakatar da shirin rage farashin Man fetur da take bayan gano wasu ‘yan Kasuwa dake amfani da wannan dama wajan cimma riba cikin gaggawa.
Matatar ta bayyana hakane a wata sanarwa wadda wakiliyar kamfanin, Fatima Dangote ta fitar.
Tace an dakatar da rage farashin man daga ranar 13 ga watan Yuli har sai abinda hali yayi.
Inda ta kara da cewa, an dauki wannan mataki ne saboda an gano wasu ‘yan kasuwar na sayarwa ‘yan kasuwar man fetur wanda basu da lasisin daukar ma a matatar Dangoten lasisinsu inda suke ciniki su samu riba cikin sauki.
Matatar tace su kuma wadancan ‘yan kasuwa idan suka dauki man suna sayar dashi ne a farasi me tsada mamakon farashin ragin da Dangoten yayi.
Sanarwar tace hakan yaudarace da kuma zagon kasa ga ‘yan kasa da kuma matatar man fetur din. Domin ana yin ragin farashin ne dan mutane su samu sauki.