
Rahotanni sun bayyana cewa, matatar man Dangote ta zarta kasar Amirka wajan kai man jiragen sama kasashen Turai a wajan Yuni daya gabata.
A watan Yunin da ya gabata, Matatar man ta Dangote ta kai Man jirgin sama Ganga 466,000 zuwa kasashen Turai wanda darajarsa ya kai Naira Biliyan N757bn.
Amma yawan wanda kasar Amurka ta kai kasashen Turan bai kai haka ba.
Wannan ba karamin ci gaba bane ga Dangoten dama Najeriya baki daya.