
Rahotanni daga jihar Osun na cewa, Wani Dansanda ya manto Bindigarsa a gidan giya a jihar bayan da yayi Mankas da giya.
Rahoton yace lamarin ya farune a Osogbo babban birnin jihar ta osun.
An bayyana sunan dansandan da wannan lamari ya faru dashi da sunan Inspector Monday.
Saidai yayi karyar cewa ya mayar da Bindigar wajan da suke ajiye makamai, saidai da aka bincika an gano karya yake.
Hakan na zuwane yayin da ake tuhumar manyan ‘yansandan Najeriya kan batan Bindigu da yawa.