
Tsohon hadimin shugaban kasa, Reno Omokri ya soki tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai bayan da ya bar APC ya koma Jam’iyyar SDP.
A wani bayani da ya wallafa a shafinsa na X, Reno Omokri ya zargi El-Rufai da rashin girmama watan Ramadana me Alfarma.
Ya bayyana cewa tun da aka kama watan Azumin Ramadana El-Rufai bai yi amfani da shafukansa na sada zumunta ba wajan fadakar da Musulmai kan watan ba, maimakon hakan sai zagi da sukar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
Sannan gashi ma a karshe ya bar Jam’iyyar APC.
Yace dan shugaban kasa, wanda ke da rabin shekarun El-Rufai yafi El-Rufai din girmama watan Ramadana dan gashinan yana bi yana tabbatar da mutanen da suka yi Azumi suna yin buda baki da kyau.