
Rahotanni sun bayyana cewa, daga shekarar 2023 zuwa 2024 kasuwanci miliyan 7.2 aka kulle suka ruguje saboda rashin tabbas na tattalin arzikin Najeriya.
Shugaban hukumar bincike akan tattalin arziki ta kasa, NESG me suna Dr. Segun Omisakin ne ya bayyana hakan.
Ya kara da cewa, hakan ya jawowa Najeriya asarar Naira Tiriliyan 94.
Ya bayyana hakane a yayin kaddamar da rahoto akan kamfanoni inda yace kaso 30 cikin 100 na kananan kasuwancin da ake dasu a Najeriya sun kulle.
Yace Najeriya na da jimullar kananan kasuwanci miliyan 24 kuma a yanzu gida Miliyan 7.2 daga cikinsu sun kulle.
Yace rashin tabbas na tattalin arziki da hauhawar farashin kayan masarufi da kashe kudi da yawa wajan gudanar da ayyukan su ne ya jawo hakan.