
Farashin ɗanyen man fetur samfurin Brent – wanda aka fi yawan ƙayyade farashi da shi a duniya – ya yi faɗuwa mafi muni cikin shekara biyar.
Faɗuwar da kusan kashi 3.2 cikin 100 – zuwa dala 63.49 kowace ganga – ta faru ne a yau Litinin da misalin ƙarfe 11:00 agogon Najeriya da Nijar.
Rabon ya yi irin faɗuwar tun watan Afrilun 2021.
Shi ma samfurin West Texas Intermediate (WTI) ya faɗi zuwa kashi 3.58, kamar yadda kamfanin labarain na Reuters ya ruwaito.
Faɗuwar farashin ta faru ne sakamakon sanarwar da Shugaban Amurka Donald Trump ya bayar ta ƙaƙaba wa dukkan ƙasashen duniya ƙarin harajin shifgar da kaya ƙasarsa.
Hakan ya sa samfurin Brent ya faɗi da kashi 10.9 cikin 100, yayin da shi ma WTI ya faɗi da 10.8.