DAGA: Abbas Yakubu Yaura
Tsòro ya mamaye tsòhon birnin Kano yayin da sarakunan biyu da ke hamayya da juna – Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da aka dawò dashi da Tsohon Sarkin Kano Aminu Ado Bayero da aka tsige suka bayyana shirinsu na yin sallar Juma’a a babban masallacin Juma’a na fadar Sarkin.
Majiyar mu ta rawaito cêwa tuni mai martaba Sarki Malam Muhammadu Sanusi II, wanda ke zaune a fadar, kuma kusa da Masallacin da ake fafatawa, ana sa ran zai jagoranci sallar Juma’a raka’a biyu.
Mai martaba Sarki Muhammadu Sanusi II zai jagòranci Sallar Juma’a a babban masallacin fadar a matsayin sarkin birnin, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Sanarwar mai dauke da sa hannun Danburan Kanò, Munir Sanusi Bayero, ta bayyana matsayar Maimartaba Sarkin Kanò Muhammadu Sanusi II zuwa Masallacin dómin jagorantar Sallar Juma’a.
An fitar da sanarwar a daren Ranar Alhamis.
Sanarwar ta Danburan ta gayyaci mazauna Kano da su zo su saurari wa’azin da Sarki Malam Muhammadu Sanusi II zai gabatar.
Sai dai kuma wata sanarwa daga wani hadimin mai martaba Sarkin, Alhaji Aminu Ado Bayero ya gayyaci jama’ar yankin da su zo tare da shi a masallacin Juma’ar na fadar Sarkin domin gudanar da sallar Juma’a.
An bayyana cewa za a fara tafiya zuwa Masallacin fadar Sarkin da karfe 12:30 na rana.
Sai dai har yanzu ‘yan sandan ba su ce uffan ba kan wannan ci gaban.