Friday, June 26
Shadow

Gawunane ya zo wajan mu dan mu bashi takarar gwamna, bamu muka nemeshi ba>>Inji jam’iyyar ADC

Jam’iyyar ADC reshen jihar Kano ta tabbatar da cewa yanzu haka ganawa na ci gaba da gudana a tsakaninta da Nasiru Yusuf Gawuna.

Shugaban jam’iyyar a jihar, Musa Ungogo ne ya bayyana haka ga manema labarai na jaridar Punchng.

Yace gawuna ya aika musu da wakilansa da suka hada da tsohon shugaban karamar hukumar Kumbotso, Alhaji Sagir Fanshekara da Hon Kadawa inda suka ce Gawuna na son komawa jam’iyyar.

Amma sai an masa alkawarin za’a bashi takarar Gwamna ba tare da hamayya ba sannan a baiwa wasu daga cikin mutanensa mukamai.

Ungogo yace sun bukaci Gawuna da ya rubuto musu da bukatunsa a rubuce su duba suga yiyuwar hakan.

Karanta Wannan  Da Duminsa: Kasa da sati daya da saukar Ganduje daga shugaban APC, Gwamnan Kano, Abba Gida-Gida zai koma APC

Yace labaran da ake yadawa a kafafen sadarwa cewa wai sune suke nemansa kuma sun masa alkawarin tikitin takarar gwamna da kudin yakin neman zabe ba gaskiya bane.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *