
Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ya ce Najeriya na da arzikin da za ta iya daukar nauyin tafiye-tafiyen da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke yawan yi zuwa kasashen waje tun bayan hawansa mulki.
Tafiye-tafiyen da Tinubu ke yi zuwa kasashen waje na shan suka daga al’ummar ƙasar duba da matsalar tattalin arziki da ake fama da ita.
Sai dai da ya ke magana a shirin ‘Politics Today’ na Channels TV, Tuggar ya ce Tinubu, sabanin korafe-korafen da ake yi, har ma yana bukatar kara tafiye-tafiyen saboda mahimmancin dabarunsa da kuma amfanin da su ke da shi ga kasar.
Ministan ya bayyana cewa, Tinubu zai iya karfafa alaka da sauran shugabannin kasashen duniya ne kawai a yunkurinsa na dora kasar nan kan turba mai kyau ta hanyar yin tattaki zuwa ƙasashen..
Ya ce, “Wannan korafe-korafen ba su da tushe. Gwamnatin nan har yanzu sabuwa ce saboda an rantsar da shugaban kasa a shekarar 2023. Ta fuskar diflomasiya, har yanzu shi ne sabon shugaban kasa. Yana buƙatar yin hulɗa da abokan aikinsa da shugabannin ƙasashe don samun damar kulla dangantaka.