Monday, December 16
Shadow

Gyaran fuska da aloe vera

Aloe Vera na gyara fatar fuska sosai inda yake kawar da dattin fuska da kara mata haske kuma idan aka duba za’a ganshi a cikin mayukan gyaran fuska da yawa.

Ga jawabin amfanin da Aloe Vera ke yiwa fata da kuma yanda za’a sarrafashi a samu abinda ake so.

Aloe Vera yana maganin duhun fata.

Yana magamin canjawar fuska da zafin rana ke kawowa.

Yana kawar da fatar data mutu a fuska wadda ke kawo duhun fuska.

Yana maganin ciwo a fuska.

Yana maganin kumburin fuska.

Yana maganin cizon kwaro irinsu sauri kudin cizo da sauransu.

Idan za’a sayi man shafawa dage dauke da Aloe vera a duba a tabbatar ba’a hadashi da giya ba ko sauran sinadarai masu kawowa fata illa.

Karanta Wannan  Gyaran fuska da manja

Babbar hanyar samun amfanin Aloe vera a fuska, shine mutum ya hada kayansa a gida.

Yanda ake hada man Aloe Vera a gida:

Za’a yanko Aloe Vera da wuka daga jikin iccensa:

Sai a wanke a bari ya bushe.

Sai a sa wuka a yanke koren jikin Aloe Vera din.

Ana iya amfani da wuka a rika karto man dake jikinsa.

Ko a sa a wani abu a matso.

Idan aka samu ruwan, kada a hada da komai a zuba a mazubi a ajiye.

Domin ajiya me kyau, a ajiye a cikin firjin.

Kamin a shafa a fuska, a fara shafawa a hannu a barshi ya dade kamin a ga idan ya nuna alamar kaikai ko canjawar kalar fata ko kuma wani reaction na daban, kada a shafa a fuska saboda kada ya lalata fuskar, idan kuma bai nuna alamar komai ba, sai a shafa a fuskan.

Karanta Wannan  Yadda ake hada sabaya

3 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *