Man kwakwa na da amfani da yawa a fuska, yana sa fuska ta yi laushi, yana maganin ciwo yayi saurin warkewa, yana kuma taimakawa wajan rage kumburi.
A wannan rubutun, zamu kawo muku amfanin man kwakwa wajan gyaran fuska.
Wani bincike ya tabbatar da man kwakwa na taimakawa sosai wajan maganin kurajen fuska da kuma yana a matsayin rigakafi dake hana kurajen fitowa mutum a fuska.
Hakanan man kwakwa na taimakawa wajan kawar da alamun tsufa a fuska.
Ana shafa man kwakwa a fuska ko jiki kamar yanda akw shafa sauran mai.
Hakanan ana cinshi da abinci.
[…] iya ajiye man a firjin. Ana amfani dashi wajan gyaran fata, gyaran fuska, gyaran gashi da kuma cin abinci ko soya kayan […]