Monday, May 26
Shadow

HASBUNALLAHU WA NI’IMAL WAKIL: Bèĺlò Țùŕjì Ya Kori Mutàñèn Gàriñ Bafàrawa

HASBUNALLAHU WA NI’IMAL WAKIL: Bèĺlò Țùŕjì Ya Kori Mutàñèn Gàriñ Bafàrawa.

Daga Datti Assalafiý

Shugaban barayin daji Be||0 Turj! ya kori mutanen dake zama a garin Bafarawa, kusan gaba daya mutanen garin sun watse zuwa neman mafaka a halin da ake ciki

Sannan Be||0 Turj! ya aika takarda zuwa ga mutanen garuruwan Kamarawa, Arume da Kagara, ya ce baya son ganin wani mutum a cikin garuruwan daga yau Lahadi zuwa misalin karfe 4 na yammaci

Akwai labarin da na gani, ance a daren jiya kadai kusan garuruwa 5 barayin daji suka yiwa hari a tsakanin jihar Katsina da Zamfara

Sannan jiya ‘yan bindiga sun kai harin ta’addanci makarantar Sakandare (GSS) dake garin Raka a karamar hukumar Tsafe jihar Zamfara inda suka kashe Malami sannan sukayi garkuwa da mutane da yawa

Karanta Wannan  Mai Martaba Sarkin Daura Ya Tunbuke Rawanin Wani Dagaci Bayan Kama Shi Da Laifin Yin Ĺàlàțà Da Wata Maťar Àurè Bayan Ya Yi Garkuwà Da ità

Abubuwan da suke faruwa a yankin Arewa na matsalar tsaro kamar babu Gwamnati a Nigeria, shin menene manufar da ta sa a yanzu Be||o Turj! yake ta tashin mutane da garuruwansu?

Ana ta zargin cewa duk garin da aka tasa a yankunan da ake fama da matsalar nan to akwai ma’adinan karkashin kasa masu daraja a garin, idan aka tada mutanen gari watakila Kasar Faransa zata mamaye gurin ta cigaba da mining kenan???

Kuma idan kun lura, ba’a so a kawar da Be||o Turj! ne, domin ba shakka akwai manyan azzalumai maciya amana da suke amfana da ta’addancinsa

Mu hadu mu kai karansu gurin Allah, duk wanda yake da hannu a wannan matsala Allah Ka dauki rayuwarsa

Karanta Wannan  Dubu Dari Biyar Rarara Ya Biya Sadakin Aisha Humaira

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *