
Ministan babban Birnin tarayya, Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa, yana da son kudi.
Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a kafar Channels TV inda yace duk wanda yace maka baya son kudi to makaryaci ne.
Wike ya bayyana cewa, babu abinda mutum zai yi ba tare da neman kudi ba a wannan zamani dan haka suna da matukar muhimmanci a rayuwar dan adam.
Wike yace ya taso gidan rufin Asiri ba zai ce masu kudi bane su sosai.