Friday, December 5
Shadow

Ji Abinda ya faru da shafukan sada zumunta na Hadiza Gabon bayan da Masoya Adam A. Zango suka sha Alwashin yin Unfollow dinta

Bayan da Hadiza Gabon ta ki saka hoton Adam A. Zango a dakin da take hira da mutane wanda ya jawo cece-kuce sosai.

Daya daga cikin matakan da masoya Adam A. Zango suka sha alwashin dauka shine zasu yi Unfollow dinta a shafukan sada zumunta dan nuna bacin Ransu.

Tun bayan shan wannan Alwashi yanzu sama da awanni 24 kenan Hutudole yana saka ido akan shafukan na sada zumuntar Hadiza Gabon dan ganin ko zata samu raguwar mabiya.

Mutane musamman a kasashen Turawa sukan dauki irin wannan mataki na Unfollow ga wani da yayi wani abinda basa so.

Saidai Hutudole har zuwa yanzu ya lura cewa Hadiza Gabon bata rasa mabiya ba ko kuma mabiyanta basu ragu ba a shafukanta na sada zumunta.

Karanta Wannan  Mutane 9 sun rasu sanadiyyar hadarin mota a jihar Jigawa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *