
Rahotanni sun bayyana cewa, an kama dan uwa a wajan Ayiri Emami wanda abokin shugaban kasa Bola Tinubu ne me suna Ajetsibo Emami sa safarar kwaya.
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA ce ta kamashi ta bakin kakakinta, Femi Babafemi inda tace an kamashi ne a Ikeja, Jihar Legas ranar 28 ga watan Yuni.
Sanarwar tace, Kasurgumin me safarar Miyagun kwayoyi ne kuma an kamashine da wasu mutane 3 dake aiki dashi.
Yace an kwacw muggan kwayoyi a hannunshi.