Wednesday, January 15
Shadow

Kalaman soyayya masu ratsa jiki da jijiyoyin

Kece Dandamalin zuciyata.

Ina sonki kuma ina fatan in aureki.

Soyayyarki na ratsa jikina kamar yanda ruwan sanyi kewa jiki idan an kwararashi yayin da ake tsaka da sanyi me tsanani.

Soyayyarki ta mamayeni kamar yanda manja ke mamaye farar jallabiya yaki fita.

Soyayyarki ta yi naso a zuciyata kamar yanda bakin mai kewa kayan bakanike me gyaran mota naso.

Na rasa ya akai zuciyata ta kamu da soyayyarki farat daya.

Ina kallonki naji cewa na hadu da kalar matar da nake son aure.

Kin yi min ta kowane bangare.

Soyayyarmu ta yi fadi ta yanda babu littafin da zai dauki bayaninta.

Karanta Wannan  Kalaman soyayya masu nishadantarwa

Ina sonki kamar ke kadaice mace a Duniya, kin zamar min sarauniyar mata wadda idan na rasata na yi babban rashin da ba zan iya maye gurbinsa ba.

Saboda soyayyar da nake miki, ko mi kika min daidaine.

Ina sonki kamar Kwai a cikin cokali.

Kafarki tana min fresh kamar in lashe.

An ce in bayyana soyayyar da nake miki amma na kasa.

‘Ya’yan mu zasu yi albarka saboda sun samo tsatso daga soyayyar gaskiya babu yaudara.

Anya zan iya yin fushi dake kuwa saboda kwata-kwata bana ganin laifinki.

Wani lokacin sai in zauna inta kallon hotonki a wayata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *