
Wani barawo ya sace wayar wata mata yayin da take tsaka da bacci.
Saidai be kashe wayar ba.
Da me wayar ta kira, sai yace zai bata amma sai ta bashi dubu hamsin.
Saidai tace masa bata da Dubu 50.
Amma tace idan yana so zata bashi kanta. Aikuwa sai ya yadda.
Tuni dai an kamashi, lamarin ya farune a Ikotun, dake jihar Lagos.