Wani matashi me suna Ishaq dake sayar da ruwa wanda aka fi sani da Pure Water a Abuja ya bayyana cewa yana da kwalin kammala Digiri mafi daraja watau First Class.
Matashin an yi hira dashi ne inda bidiyon hirar ta watsu sosai a kafafen sada zumunta.
Yace tun da ya kammala karatun bashi da aikin yi.
Saidai Tuni wata baiwar Allah ta bukaci da a nemo mata shi dan ta taimaka masa.