
Jigo a jam’iyyar APC ya bayyana cewa, zasu ci gaba da ganin cewa sun yi dukkan mai yiyuwa dan tarwatsa jam’iyyar ADC.
Yace ADC ta kwace musu Malam Nasiru Ahmad El-Rufai, da Abubakar Malami, da Rotimi Amaechi dan haka ba zasu zuba ido su gansu sun yi nasara ba.
Yace Kuma suna ADC din yasan suna nasu kokarin wajan gurgunta jam’iyyar APC dan haka suma zasu yi iya nasu kokarin.
Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Arise TV.