Matar marigayi Sheikh Albani Zaria ta fito ta yi cikakken bayani kan matsalar da suke ciki game da ‘yan damfara da kuma daliban malamin.

A wani Bidiyo da ya yadu sosai a kafafen sada sumunta, an ga me dakin Albani tana zubar da hawaye saboda bakin cikin da ta samu kanta a ciki.
Da yawan mutane sun tausayawa iyalan malam inda aka rika tambayar ina dalibansa da sauran malamai ‘yan uwansa?