
Mahukunta a jihar Taraba sun kama wani basaraken jihar da karbar Naira Miliyan 1.5 ya baiwa ‘yan Bindiga mafaka a masarautarsa.
Mutane 23 ne aka kama ciki hadda wasu mata 4 wanda ake zargin basarakenne ke basu mafaka.
Basaraken ya karbi kudinne dan baiwa ‘yan Bindigar mafaka, kamar yanda sanarwar ta tabbatar.
Sojoji sun kashe daya daga cikin ‘yan Bindigan da kuma kwati makamai ciki hadda Bindigar AK47.
Lamarin ya farune ranar Lahadi, 2 ga watan Janairu a kauyen Angwan-Bala dake kamar Hukumar Karim Lamido ta jihar.
Kakakin rundunar sojin dake jihar ta taraba, Captain Oni Olubodunde ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace ‘yan Bindigar sun tserone daga jihar Filato inda suka nemi mafaka a wajan basaraken.