
Biyo bayan Tuntuben da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya yi ya fadi a kasar Turkiyya, yayin da yake tafiya shi da shugaban kasar Turkiyyan Recep Erdogan.
Fadar shugaban kasa ta fitar da sanarwar cewa, shugaba Tinubu yana cikin koshin Lafiya.
Sanarwar wadda ta fito daga bakin me magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya bayyana cewa, yanayin yanda aka shimfida kafet din da shugaba Tinubu ke tafiya akai ne bai shimfidu da kyau ba shiyasa yayi Tuntuben.
Sanarwar tace shugaba Tinubu bai ji ciwo a faduwar da yayi ba, kuma yanzu haka ya ci gaba da ziyarar aikin da yake a kasar ta Turkiyya.