Friday, June 26
Shadow

Kalli Bidiyon: Da gaske Hadiza Gabon ta yi martani bayan zargin soyayya da Saleem Goje?

Bidiyo na ta yawo a kafafen sada zumunta inda akw rade-radin cewa, wai Hadiza Gabon ta yi martani bayan zargin da matar Saleem Goje ta yi cewa yana soyayya da ita.

Wani Bidiyo daya nuna Hadiza Gabon na kame-kame ya karade kafafen sadarwa inda ake cewa wai shine na martanin Hadizar.

Saidai Bincike da Hutudole yayi ya gano cewa ba gaskiya bane, Har yanzu, Hadiza Gabon bata yi martani ba kan wannan zargi da aka mata.

Hasali ma tun bayan bayyanar labarin, Hadiza bata kara yin wallafa a shafinta na sada zumunta ba.

Karanta Wannan  NAFDAC sun kulle shagunan dake sayar da magungunan jabu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *