Saturday, July 25
Shadow

Kalli Bidiyon: Daliban Marigayi Dr. Idris Dutsen Tanshi sun nesanta kansu da Malam Abdulrahman Umar Sautussunnah, sunce baya cikin koyarwar Dr. Idris zama da matan mutane wai da sunan wa’azi

Daliban Marigayi, Dr. Idris Dutsen Tanshi sun fito sun nesanta kansu da Malam Abdulrahman Umar Sautussunnah inda suka ce ba dalibin malaminsu bane.

Sannan sun ce abinda yake yadawa a kafafen sada zumunta da kuma zama da ya kanyi da matan da ba nasa ba wai da sunan wa’azi, ba koyarwar Dr. Idris bace.

A baya dai an ga Malam Abdulrahman Umar Sautussunnah tare da malama Juwairiyya zaune a kujera daya kusa da juna inda Bidiyon ya jawo cece-kuce sosai.

Hakanan a kwanannan ya wallafa Bidiyon tare da wata a kusa dashi tana karatun Qur’ani wanda shima ya jawo cece-kuce wasu na cewa matarsa ce wasu na cewa kanwarsa ce.

Karanta Wannan  'Yansanda sun kama Jarumar Fina-Finan Hausa, Khadija MaiNumfashi an tafi da ita Legas

Malam Abdulrahman Umar Sautussunnah dai yakan kawo labaran wasu abubuwan ban mamaki da yakance an kawo masa tambaya akai wanda sukan jawo cece-kuce.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *