
Affan Buba Abuya ya bayyana cewa, yayi aiki tare da Farfesa Sheikh Isa Ali Pantami har sau biyu, a yayin da yana shugaban ma’aikatar NITDA da kuma Minista.
Yace Malam na da ilimin addini amma bashi da mu’amala me kyau.
Yace dalili ma da yasa kenan yace ba zai goyi bayansa da ya fito takarar Gwamnan jihar Gombe ba.
Yace Pantami mutane kan so su ganshi lokacin yana Minista amma sai yaki, yace har rana aka ware ta ganawa da mutane amma daga baya yace a daina, yace duk sanda yake son ganawa da wani zai gaya masa.
Yace idan zasu je Gombe yakan cewa Malam a tanadi kudi da za’awa mutane hidima amma sai malam yace bai yadda ba.
Yace daga aljihunsa yakan cirewa ya bayar da sunan malam.