
Rahotanni sun bayyana cewa, kasashe da yawa ciki hadda India sun ki amincewa da jakadun da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya aika musu.
Kasar ta India tace dalilinta na kin amincewa da jakadun na shugaba Tinubu shine wa’adin mulkinsa ya kusa karewa.
Wata majiya daga fadar shugaban kasar tace ba India kadai bace, kasashe da dama sun nuna alamun kin amincewa da jakadun.
Dalili shine suna tunanin idan shugaba Tinubu bai ci zabe ba a 2027 akwai yiyuwar sabon shugaban kasar da ya hau zai iya canja jakadun.
A kwanan nan ne dai shugaba Tinubu ya nada jakadu guda 65