
Rahama Kumo ta bayyana cewa wata Kirista ta kirata take ce mata zata musulunta saboda ta samu miji Musulmi yace zai aureta.
Rahama wadda Tauraruwar Tiktok ce dake magana akan auratayya tace ta hana wannan kiristan karbar Musulunci.
Tace dalilinta shine ta gayaa Kiristan cewa idan dai saboda wannan musulmin mijinne zata musulunta to kada ta musulunta
Tace amma idan Saboda addinin musulunci ya mata ne tana son shiga to tana iya musulunta.
Tace dalili shine akan yi irin wannan aure daga baya a saki matar wasu ma hadda yara wasu kuma ba’a dadewa ma abin ya zo su koma ruwa wasu kuma aita wahala dasu.