
An zargi mawaki Soja Boy da yin kalaman Rashin da’a ga fiyayyen Halitta, Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam).
Soja Boy yayi maganar ne a wani Tiktoklive yayin da yake mayar da martani game da lamarin da ya faru a masallacin Sheikh Musa Lukuwa.
A cikin jawabin nasa an ji yana ta bayyana Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) da kalmar “Wani”
Da yawa sun rika tambayar Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) din yake cewa wani?