
Wasu Sanatocin Najeriya sun fara bude idanu suna gayawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu gaskiya.
Daya daga cikin sanatocin shine Sanata Monguno.
Sanata Monguno ya zargi cewa duk da tsawaita kasafin kudin shekarar 2025 amma Gwamnatin tarayya bata baiwa Bangaren tsaro kudin komai ba.
Yayi barzanar cewa, idan ba’a bayar da wadannan kudade ba, zai kai kudirin doka zauren majalisa na tsige shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
Sanata na biyu shine, Sanata Adamu Aleiro.
Sanata Aleiro yace yawan bashin da gwamnati ke ciyowa yayi yawa.
Sanatan yace Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnatin Tinubu ta ciwo bashin Naira Tiriliyan 80.
Sannan ya koka da cewa har yanzu ba’a fara aiwatar da kasafin kudin shekarar 2026 ba.