
Tauraruwar fina-finan Hausa, Amal Umar ta dauki hankula a kafafen sada zumunta bayan da aka ga Bidiyon ta tare da Usman Uzee inda suke kame-kamen hannu da wasanni irin na ma’aurata.
A karshen Bidiyon dai an ga yanda Usman Uzee ya daga Amal Umar sama cak ya tafi da ita daki.
Lamarin ya jawo cece-kuce inda aka rika sukar musamman Amal Umar saboda Usman ba kowane ya sanshi ba amma shima dan Arewa ne daga jihar Kaduna.
Da yawa sun bayyana cewa irin wannan fim din ya sabawa Addini mda al’adar mutanen Arewacin Najeriya.