
Wannan wani dan Najeriya ne dake zaune a kasar Ingila me suna Ugo, wanda ya kama matarsa da wani Kwarto da ta kai gida.
Ya bayyana takaicinsa a kafafen sada zumunta inda ya bayar da labarin cewa, shine ya dauki nauyin kai matar tasa kasar Ingila sannan ya sai mata mota sannan shi ke biyan kudin makarantarta.
Yace amma duk wannan bai hana taci amanarsa ba.
Ya nuna Bidiyon lokacin da ya sai mata motar.
A karshe dai yace ya rabu da ita.