
Mataimakin Gwamnan jihar Zamfara, Mani Malam Mamman ya sha da kyar a hannun matasan kauyen Gwashi dake karamar hukumar Bukkuyum na jihar ta Zamfara.
Yaje ne yi musu jajen matsalar tsaron dake damunsu.
Saidai lamarin bai kare da kyau ba dan guduwa yayi.
Har jami’an tsaronsa ma sun tsere sun bar motarsu daya a kauyen.