
An ga Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima akan hanyarsa ta zuwa taron Majalisar Dinkin Duniya a Birnin New York City na kasar Amurka ya tsaya ya gaisa da wani dan Najeriya dake tsaye a gefen titi.
Dan Najeriyar yayi ta tsalle yana murna da faruwar hakan.
Saidai wasu na cewa, da a Najeriya ne da hakan ba zata faru ba.