
Wannan wani magidanci ne da ya bayyana cewa, baya son tallafin kayan abinci da za’a bashi muddin sai an daukeshi hoto.
An ga yanda ya dakatar da me daukar hoton inda yace baya son kayan abincin.
Da yawa sun jinjina masa inda suka ce ya kwatarwa kansa mutunci.