Monday, August 3
Shadow

Kalli Bidiyon: Yanda yaran Rarara sukawa Mansurah Isah Dibar Albarka suka fitar da update dinta

A yayin da ake yakin cacar baki tsakanin Tauraruwar fina-finan Hausa, Mansurah Isah da Rarara da Matarsa A’ishatulhumaira bayan da Mansuran ta fita daga Tafiyar Triple R.

Wasu mata yaran Rarara sun fito sun saki Update din Mansurah Isah.

A baya dai Mansurah Isah ta fice daga tafiyar Rarara ta Triple R, saida wasu Rahotanni sun fito sun bayyana cewa ta koma tafiyar.

Saidai Kwatsam ana kan hakane sai ga Mansurah Isah ta sake fitowa tace ta bar Tafiyar Rarara ta Triple R kuma ta musu alkawarin ba zata yi hira da ‘yan jarida ba.

Tace amma taga ana tura yara suna mata rashin Kunya a kafafen sadarwa inda ta gargadi Rarara da matarsa A’ishatulhumaira inda tace idan aka fara tone-tone abin ba zaiwa kowa dadi ba.

Karanta Wannan  Yaron Sojannan da muka lara dashi jiya sam bai da Kunya ga girman kan tsiya>>Inji Ministan Abuja, Nyesom Wike

A’ishatulhumaira, matar Rarara ta mayarwa da Mansurah Isah da martanin cewa, Ita menene nata a ciki da zata rika sakata a cikin zancenta?

Saidai bayan wanan, Sai ga Usman wanda yake ikirarin cewa shine Sarkin Yakin Rarara ya fito yace Rarara yaso yawa Sani Musa Danja Magana ya mayar da Mansurah Isah dakin Mijinta.

Yace a lokacin da Rarara ya fadi wannan maganar, Saida Mansurah Isah ta tashi tsaye taita tafi saboda jin dadin hakan.

Yace amma yanzu tunda ta zabi ta barsu, to A haka zata mutu ba zata yi aure ba.

Hakanan sai kuma ga wasu ‘yan mata yaran Rarara da suka fito suka bayyana cewa wai da aka je wajan Me baiwa shugaban kasa shawara akan harkar tsaro, Malam Nuhu Ribadu da Mansurah Isah, ta tashi tsaye take cewa Nuhu Ribadu ya ganeta kuwa? Itace Mansurah Isah, Matar Sani Danja, amma Nuhu Ribadu yace bai gane ta ba.

Karanta Wannan  Ni gadon Musulunci na yi wajan iyayena, amma matata Fasto ce kuma ban taba ce mata ta zama Musulma ba>>Inji Shugaba Tinubu
https://www.tiktok.com/@babynice_yargaske/video/7661354141704670472?_r=1&_t=ZS-97xvn8S31RU

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *