Friday, June 26
Shadow

Kalli Bidiyon: ‘Yar Najeriya dake biyan kudin hayar gidan da take zaune a Lagos Naira Miliyan 50 duk shekara ta dauki hankula

Wata ‘yar Najta dauki hankula a kafafen sadarwa bayan data koka da cewa me gidan da take haya ya mata karin kudin haya.

Matar ta fito tana kokawa inda tace me gidan yana son ya tashe ta daga gidan saboda yana son kara kudin hayarsa kuma karin da zai yi yasan yana da yawa ba lallai ta yadda ba.

Tace ya tashi mutane da yawa daga gidan saboda su shidane a gidan amma da ya zo kanta sai ta rokeshi har ta samu wani da ya sani dan ya sa baki.

Sai yace mata amma saidai idan zata yadda da sabon kudin hayar da zai saka.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo Yanda wannan matar ke aikin da ake biyanta Naira Dubu 40 duk bayan awa daya

Tace ta amince inda a baya tana biyan wajan Miliyan 20 a shekara, yanzu kuma aka mayar dashi Miliyan 50 a shekara.

Tace duk da haka tace ta amince amma sai ya ci gaba da matsa mata sai ta tashi daga gidan sannan har ya cire mata wutar Lantarki daga gidan.

Ta dai nemi Hukumomi da su shiga lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *