Wednesday, January 15
Shadow

Kalli Hotuna da bidiyon kisan wulakancin da ‘yan I-POB masu son kafa kasar Biafra sukawa sojojin Najeriya sannan suka kona motar sojojin a jihar Abia

Rahotanni sun bayyana cewa, wasu da ake kira da ‘yan Bindigar da ba’a sansu ba, watau Unknown Gunmen, amma ana kyautata zaton ‘yan kungiyar IPOB ne dake son kafa kasar Biafra sun kashe sojoji 2 a jihar Abia.

Sun kashe sojojinne a wani shingen sojojin dake Obikabia jihar ta Abia a ranar tunawa da wadanda suka yi yakin Biafra.

A wani bidiyo dake ta yawo a shafukan sada zumunta, an ga ‘yan Bindigar bayan sun kashe sojojin suka kuma kona motarsu kurmus.

Kalli Bidiyon a kasa:

Tuni dai gwamnonin jihohin Inyamurai suka fito suka yi Allah wadai da lamarin tare da nesanta kansu dashi

Karanta Wannan  Wani mutum da aka yi wa duka saboda zargin wulakanta Ƙur'ani a Pakistan ya rasu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *