
Wata budurwa ta tsallake rijiya da baya biyo bayan bin saurayinta da ta yi zuwa Otal.
Budurwa ta hadu da saurayinne a kafar sada zumunta inda ya bayyana mata cewa shi ma’aikacin kamfanin man fetur ne inda suka yi mahada a wani Otal dake Abuja.

Masu otal din sun bayyana cewa, mutumin ya bayyana sunansa da cewa, shi Emmanuel Okoro ne kuma daga jihar legas yake.
Ita kuma budurwar sunanta Promise Eze daga jihar Ebonyi.

An isketa a dakin Otal daure a jikin kujera bayan da ma’aikatan Otal din suka kira ‘yansanda.
Bayan da aka kwaceta aka kaita Asibiti ta dawo hayyacinta, ta bayyana cewa mutumin ya ce mata sunansa, Michael Prince.

Kakakin ‘yansandan babban birnin tarayya, Abuja, SP Josephine Adeh ta tabbatar da faruwar lamarin inda tace suna kan neman wanda ake zargi ruwa a Jallo.